Colombia ta nemi afuwar Sudan kan yadda sojojin hayar ƙasar ta ke taimaka wa RSF

Colombia ta nemi afuwar Sudan kan yadda sojojin hayar ƙasar ta ke taimaka wa RSF

Ministan harkokin wajen Colombia Luis Gilberto Murillo ne  ya nemi afuwar, a lokacin wata ganawa da suka yi da takwaransa na Sudan Ali Yusuf ta waya.

Gilberto ya nuna damuwarsa tare da Allah wadai kan yadda ƴan ƙasarsu suke taimakawa sojojin RSF, inda ya jadda aniyar gwamnatin ƙasar na ganin ta warware lamarin cikin ruwan sanyi tare da maidasu gida.

A nasa tsokacin, ministan harkokin wajen Sudan Ali Yusuf,  ya ce abin takaici ne yadda aka samu ƴan ƙasar Colombia da ke yaƙar al’ummar Sudan.

Ya jadda aniyar Sudan ta ganin sun yi aiki tare da Colombia wajen kare sake faruwan hakan a nan gaba, da kuma kare alakar da ke tsakanin ƙasashen biyu.

Kafin ganawar da ministocin harkokin wajen ƙasashen suka yi ta waya dai, sai da jakadar Colombia a Masar Anne Melania de Gaviria ta gana da takwaranta na Sudan da ke Masar din Emad-Eddin Mustafa Adawi, inda ta nuna kaɗuwarsu kan yadda aka samu mutanen ƙasarsu da ke taya RSF yaƙi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)