Cholera da yunwa sun sake ɗaiɗaita mutanen da yaƙi ya tagayyara a Sudan

Cholera da yunwa sun sake ɗaiɗaita mutanen da yaƙi ya tagayyara a Sudan

Daraktan hukumar WHO a jihar Port Sudan Shible Sahbani ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa daga ranar 22 ga watan Yulin da ya gabata an samu mutane 658 da suka harbu da cutar ta cholera ko kuma amai da gudawa musamman a jihohin ƙasar 5.

Jami’ar ta bayyana cewa sakamakon yadda yaƙi ya ɗaiɗaita kusan dukkanin ɓangarorin kiwon lafiyar ƙasar kai tsaye cutar kan kashe kusan dukkanin waɗanda suka kamu saboda rashin kulawa.

Sahbani ta ce yanzu haka akwai mutane dubu 200 da ke cikin haɗarin kamuwa da cutar, a wani yanayi da ƙarancin abinci ke ci gaba da ta'azzara yunwar da al'ummar ƙasar suka tsinci kansu a ciki musamman yankunan da rikicin ya fi tsananta.

Bayanai na nuna cewa matsananciyar yunwar na daga cikin dalilan da suka haddasa tsanantar cutar ta Cholera lura da yadda jama'a ke cin duk abin da suka samu kawai don kawar da yunwar da ke addabar su.

Yaƙi tsakanin Sojin Sudan da dakarun kai ɗaukin gaggawa na RSF ya jefa ƙasar a mafi munin tagayyara baya ga raba mutane fiye da miliyan 10 da muhallansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)