
Tsohon Firaministan ƙasar ta Mali ya bayyana damuwa da rashin gamsuwa da yaɗa majalisar sojin ƙasar ke tafiyar da shugabanci tun bayan da aka sauke shi daga mukamin Firaminista.
Rikicin da ya barke tsakanin gwamnatin mulkin soji da ’yan siyasa masu neman sauyi da suka hada kai wajen kawo ƙarshen shugabancin tsohuwar gwamnati.
Wannan shi ne babban sakon Choguel Maïga a ganawarsa ta farko da manema labarai tun bayan korar da aka yi masa a watan Nuwamban 2024.
Tsohon Firaministan a siyasance, yana kan manufarsa na tafiyar da lamuransa a fuskar siyasa ba tareda nuna shakku ko fargaba, Choguel Maiga ya dauki matsayin dan adawa ya kuma yi tir da kamun yan siayasa da aka yi ba bisa ka'ida ba, kafin ya nemi gwamnatin mulkin soja da ta kara yin tsauri da nuna gaskiya a harkokin tafiyar da al'umma, da samar da sharuddan komawa ga tsarin mulkin kasa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI