China za ta samar da guraben ayyuka miliyan guda a nahiyar Afrika

China za ta samar da guraben ayyuka miliyan guda a nahiyar Afrika

Ƙasar ta biyu mafi ƙarfin tattalin arziƙi na shirin faɗaɗa zuba jarinta ga nahiyar mafi saurin haɓaka wadda kuma ke matsayin babbar kasuwa ga China wajen baje hajar cinikayyarta ta yadda ɓangarorin biyu ke shirin buɗe wani sabon babin alaƙa da zai kai ga samar da ayyukan yi ga ɗimbin al’ummar nahiyar.

Matsayar da China ta sauya daga babbar mai bayar da bashi zuwa mai zuba jari wajen bunƙasa kamfanoni don samar da guraben ayyuka a ƙasashen na nahiyar Afrika, ya bada tabbacin ci gaban da ake samu tsakanin ɓangarorin biyu na ƙasar ta Asiya da ƙasashen nahiyar Afrika.

Fiye da wakilcin ƙasashe 50 daga nahiyar Afrika ne ke halartar taron ƙarfafa hulɗa tsakaninsu da China, bayan makamancinsa a bara waccan da ya kai ga cimma alƙawarin ganin ƙasar ta Asiya ta sayi kayaki daga ƙasashen na Afrika da darajarsu ta kai biliyan 3.

Xi Jinping ya shaidawa shugabannin ƙasashen na Afrika cewa China za ta gudanar manyan ayyuka 30 a ƙasashe masu arziƙin ƙarƙashin ƙasa baya ga bayar da tallafin yuan biliyan 360 dai dai da dalar Amurka biluyan 50 da miliyan 700.

Xi jinping ya ce a koda yaushe China na fatan ƙarfafa alaƙa ne zuwa matakin ƙololuwa tsakaninta da nahiyar Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)