Bayan kammala taron miƙa sansanin sojin Faransa na ƙarshe ga gwamnatin Chadi, Deby ya gana da sojojin ƙasar da jami’an diflomasiyya a wani taro da ya gudana a babban birnin ƙasar, N’Djemena.
Miƙa sansanin na ƙarshe wato Kossei da ke N'Djamena ga gwamnatin Chadi ya tabbatar da kawo ƙarshen yarjejeniyar tsaro da Chadi ta yi da tsohuwar uwar gijiyarta Faransa a watan Nuwamba.
Deby ya faɗa a sansanin da yanzu iya tutar ƙasarsa ce ke kaɗawa, cewa ba wai sun yanke alaƙa baki ɗaya da Faransa bane, sai dai iya ta tsaro ce kawai suka yanke.
Ya ƙara da cewa dole ne Chadi ta ƙara ƙarfafa tsaronta tare da ƙulla sabbin yarjejeniyoyi da bangarorin da za su mutunta juna, ba tare da sadaukar da ƴan cin kanta ba.
Sojojin Faransa sun shafe gwamman shekaru a Chadi tun bayan samun ƴan cinta a shekarar 1960, inda suka taimaka wajen bayar da horo ga sojinta.
Ƙasar Senegal ma na shawarar katse hulɗar tsaro da Faransa nan da ƙarshen shekarar 2025 da muke ciki, yayin da Faransa ta rage yawan dakarunta da ke Ivory Coast da Gabon.
Koda yake ƙasashen Mali , Nijar da Burkina Faso sun tilastawa sojojin Faransa ficewa daga ƙasashensu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI