Chadi ta sanar da kawo karshen yarjejeniyar hadin gwiwar tsaro da Faransa

Chadi ta sanar da kawo karshen yarjejeniyar hadin gwiwar tsaro da Faransa

Ministan harkokin wajen Chadi Abderaman Koulamallah ya bayyana haka a shafin sada zumunta na ma'aikatar harkokin wajen kasar cewa "Gwamnatin Jamhuriyar Chadi ta dau matakin kawo karshen yarjejeniyar hadin gwiwar tsaro da ta kulla da Faransa."

Kasar Chadi dai ita ce kasar da ta rage a yankin Sahel da sojojin Faransa ke ci gaba da zama, wadda ta zama sansani na karshe tun bayan ficewar sojojin Farnsa daga Nijar, Mali da Burkina Faso.

"Faransa muhimmiyar abokiya ce amma kuma dole ne a yanzu ta yi la'akari da cewa Chadi ta girma,kuma Chadi kasa ce mai cin gashin kanta kuma tana kishin ikonta," kalaman Ministan harkokin wajen kasar na Chadi Koulamallah,wanda ya kasance a ganawar da shugaban na Chadi ya yi da shugaban diflomasiyyar Faransa Jean-Noel Barrot.

A yan shekaru da suka gabata kasar ta Chadi ta fuskanci rashin tsaro daga yan tawaye,wanda a baya dai Cahdin ta yi dogaro da goyon bayan sojojin Faransa don fatattakar su a shekarun 2008 sannan a cikin 2019.

Ministan harkokin wajen Chadi da babbar murya, Koulamallah ya tabbatar wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP, cewa kusan sojojin Faransa dubu daya ke girke a kasar yanzu haka.

 Ya zuwa wannan lokaci hukumomin na Chadi bas u bayar da lokacin da Faransa za ta janye dakarun ta  a kasar ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)