Chadi ta sanar da hallaka mayaƙan Boko Haram kusan 300

Shugaban ƙasa Mahamat Idris Deby ya bada umarnin kaddamar da yaƙin akan mayakan boko haram, bayan wani kazamin harin da suka kai sansanin sojin ƙasar wanda ya laƙume rayukan dakaru 40.

Janar Chanane Issakha Acheik, mai magana da yawun rundunar sojin ƙasar ya shaidawa manema labarai cewar mayaka 297 suka kashe a ƙarƙashin rundunar Haskanite, yayin da su kuma suka yi asarar sojoji 24 da fararen hula guda 4.

Babu adadin sojoji 40 da aka kashe a sansanin Ngouboua dake iyaka da Najeriya a sabon adadin da kakakin sojin ya gabatar.

Shugaba Deby da kansa ya jagoranci ƙaddamar da akan mayakan na makwanni 2, sanye da kayan soji.

Ƙasar Chadi na ɗaya daga cikin ƙasashe 4 a Ƴankin Tafkin Chadi dake yaƙi da boko haram na sama da shekaru 10 da suka gabata, tun bayan fantsamar su daga Najeriya.

Wannan rikicin dai ya yi sanadiyar hallaka mutane sama da 40,000 a ƙasashen guda 4, tare da raba sama da miliyan 2 daga muhallin su.

Rahotanni sun ce yanzu haka masana yadda ake sarrafa jiragen sama marasa matuka na soji daga Turkiya na Chadi domin horar da dakarun ƙasar akan yadda za su yi amfani da na'urorin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)