A cikin wata sanarwa da kakakin gwamnatin ƙasar Abderaman Koulamallah ya fitar, ta ce bayaga sojojin da aka kashe, wasu ƙimanin 20 sun samu raunuka.
Sao’i bayan kashe sojojin, shugaban ƙasar Mahamat Idriss Deby Itno, ya ƙaddamar da wani sintiri na bin diddigin maharan.
Ofishin jakadanci Faransa da ke Chadi, ya wallafa wata sanarwa da ke tabbatar da goyon bayansu ga ƙasar wajen yaki da ta’addancin da ta ke yi.
Ƙasar ta Chadi dai ta bada hutun kwanaki uku da aka fara daga jiya Talata, tare da sassauto da tutoci da kuma hana gudanar da duk wani biki, don nuna jimami da kuma girmama sojojinta da ta rasa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI