Chadi ta musanta kai hare-hare kan fararen hula a yankin tafkin Chadi

Chadi ta musanta kai hare-hare kan fararen hula a yankin tafkin Chadi

A ranar Alhamis da ta gabata ne masunta na cikin gida da kungiyoyi suka zargi Chadi da kashe "dama" daga cikin masunta a Najeriya da nufin kai wa mayakan Boko Haram hari a yankin tafkin Chadi.

Dakarun Chadi Dakarun Chadi © AFP

Wani babban jami'in kasar Chadi wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya tabbatarwa kamfanin dilancin labaren AFP cewa, harin da aka kai a tsibirin da ke kan iyakokin Najeriya da Nijar,ya kasance wani wuri da “yan Boko Haram ke cudanya da masunta da manoma a duk lokacin da suka aikata laifukansu saboda haka yana da wuya a bambanta  jama’a da ‘yan ta’adda,a cewar wannan jami'i.

Rahotanni sun tabb atar da cewa wani jirgin saman sojan kasar Chadi ya kai hari kan masunta a tsibirin Tilma, inda ya kashe masunta da dama," in ji Babakura Kolo, shugaban kungiyar masu yaki da 'yan Boko Haram a Najeriya ranar Alhamis.

Babakura ''ya ci gaba da cewa "Jirgin ya danganta masunta da 'yan ta'addar Boko Haram da suka kai hari a sansanin soji a Chadi ranar Lahadi."

Wasu daga cikin dakarun Chadi a yankin tafkin Chadi Wasu daga cikin dakarun Chadi a yankin tafkin Chadi © AP

Wani mai kamun kifi Sallau Arzika ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP cewa "Jirgin na yaki ya yi wa Tilma kawanya kafin ya fara jefa bama-bamai yayin da mutane ke gudu ta ko'ina domin neman mafaka."

A cikin dare daga ranar Lahadi zuwa litinin mayakan Boko Haram sun kai wani samame a wani sansanin soji dake yankin tafkin Chadi. Adadin wadanda suka mutu ya kai 40 daga cikin dakarun Chadi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)