Masu yaɗa farfagaandar manufofin Rashar, Maksim Shugaley da Samir Seifan waɗanda ke da kusanci da ƙungiyar sojojin hayar Rasha ta Wagner, an tsare su ne jim kaɗan da saukar su a filin jirgin sama na N’djamena a ranar 19 ga watan Satumba kamar yadda Ma’aikatar Diflomasiyar Rasha ta tabbatar.
Kamfanin Dillacin Labaran Rasha RIA ya rawaito cewa a ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne jami’an shige da ficen Chadi suka kama mutanen bayan an shaida musu cewa, ba su da izinin shiga ƙasar kafin daga bisani a nemi su a rasa.
Sau biyu masu yaɗa farfagandar ke kai ziyara a N’djamena a bara ba tare da sun fuskanci matsala ko guda ba.
Offishin Jakadancin Rasha a Chadi ya ce yana ci gaba da tuntubar mahukuntan ƙasar domin samun ƙarin haske game da tsare mutanen.
Wannan kamen na zuwa ne a yayin da alaka da ke tsakanin ƙasashen biyu ke ci gaba da samun tagomashi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI