Chadi ta fara neman taimakon ƙasashe bayan ambaliya ta kashe mutane 70

Chadi ta fara neman taimakon ƙasashe bayan ambaliya ta kashe mutane 70

Ministan cikin gidan ƙasar Mahamar Assileck ya yi wannan kira inda ya ke cewa halin da yankin Tibesti ke cewa dama sauran sassan da ambaliyar ta shafa abin damuwa ne matuƙa wanda ya tilasta gwamnati neman agajin ƙasashe.

Chadi na ci gaba da fuskantar illoli masu tarin yawa bayan saukar ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a baban birnin ƙasar da wasu sauran larduna, ko da ya ke lamarin ya fi tsananta a yankin Tibesti inda ambaliya ta faro  tun a rana 9 ga watan Augusta.

Sai dai hukumomin yankin da kungiyoyin fararen hula sun bayyana damuwa kan rashin kawo dauki ga mutanen da lamarin ya shafa.

Duk da cewa an samu yankewa ruwan a rana 18 ga wannan watan, adadin wadanda suka mutu ya zuwa yau ya haura sama da mutum 70 a yankin na Tibesti.

Wani da lamarin  ya rutsa dashi ya bayanna cewa suna cikin matukar damuwa bayan da ambaliyar ruwan  ta yi awon gaba da komai, inda ya bayyana cewa ibtila'in ya shafi hatta asibitocin da ke yankin.

Kantoman yankin Aouzou a Tibesti, ya yi kira ga kungiyoyi gaji da su kawo dauki, bayan da karfin ruwan ya tone dubban nakiyoyin da aka ɗana yayin yake-yaken da yankin ya fuskanta a shekarun  baya. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)