Chadi ta daƙile harin da ƴan ta'adda suka kai fadar shugaban ƙasa

Chadi ta daƙile harin da ƴan ta'adda suka kai fadar shugaban ƙasa

Kakakin gwamnatin Chadi Abderaman Koulamallah ya ce maharan 24 ne suka farwa fadar kuma dakarun Sojin ƙasar sun hallaka 18 daga cikinsu, ko da ya ke suma sun kashe jami’i guda.

Koulamallah ya ce baya ga mutanen 19 da suka mutu yayin musayar wuta tsakanin Sojin ƙasar da maharan akwai kuma wasu mutum 6 daga ɓangaren maharan da kuma 3 daga ɓangaren jami’an tsaron Chadi ciki har da wani da ke cikin mawuyacin hali.

Ginin fadar shugaban ƙasar Chadi na Djambel Bahr a birnin Ndjamena. Ginin fadar shugaban ƙasar Chadi na Djambel Bahr a birnin Ndjamena. © David Baché

Sa’o’i ƙalilan bayan harin ne Koulamallah ya fito a wani bidiyo da aka yaɗa kai tsaye ga al’ummar ƙasar, inda ya ke zagaye da Sojoji ɗaure da bindiga a ɗamararsa ya na sanar da daƙile yunƙurin kai harin fadar shugaban ƙasa.

Harin na zuwa a dai dai lokacin da ministan harkokin wajen China Wang Yi ke ziyarar aiki a Chadin, kuma jim kaɗan bayan ganawarsa da shugaba Mahamat Idris Deby wanda ke cikin fadar lokacin faruwar harin.

A shekarar 2021 ne Mahamat Deby ya ƙarbi ragamar ƙasara matsayin shugaban riƙon ƙwarya bayan mutuwar mahaifinsa a fagen dafa yayin karan batta da ƴan tawaye, jagoran da ya fara mulkar Chadi tun bayan juyin mulkin da ya yi a shekarun 1990.

Wasu majiyoyi sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa Boko Haram ce ta ƙaddamar da harin kan fadar shugaban ƙasar na Chadi sai dai Koulamallah ya ce maharan ba Boko Haram ba ne haka zalika ba ƴan tawaye ba ne, face wasu wawayen mashaya.

A gefe guda wata majiya ta shaidawa Reuters cewa, harin ka iya zama na ta’addanci.

Wasu ganau sun ce tun farko motoci 3 ne suka tsaya a ginin gab da fadar shugaban ƙasar kuma nan ta ke suka fara harbe-harbe sai dai cikin gaggawa Sojoji suka daƙile barazanar tasu.

Sojojin Chadi kenan, yayin da suke aikin sintiri a birnin N'Djamena. Sojojin Chadi kenan, yayin da suke aikin sintiri a birnin N'Djamena. AP - Jerome Delay

Mazauna yankunan sun ce sun jiyo ƙarar harbe-harbe na tsawon lokaci gabanin lafawarsu a gab da fadar shugaban na Chadi.

Harin dai ya zo ƙasa da makwanni 2 bayan Chadi ta gudanar da babban zaɓenta haka zalika kwanaki ƙalilan bayan ficewar Sojin Faransa daga ƙasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)