Chadi ta ce an kyale ta ita kadai tana yakar 'yan ta'adda a Tafkin Chadi

Chadi ta ce an kyale ta ita kadai tana yakar 'yan ta'adda a Tafkin Chadi

Wannan dai ya biyo bayan wani kazamin harin da aka kai a karshen watan Oktoba inda ‘yan ta’addan suka kai hari a wani barikin tafkin Chadi, lamarin da ya yi sanadin rayukan sojoji kusan 40.

Kan hakan ne, shugaban kasar ya kaddamar da shirin yaki da mayakan karkashin rundunar Haskanite.

Hukumomin kasar sun tabbatar da kisan mayakan kungiyar ta’addancin kusan 100.

Gwamnan lardin tafkin du Lac, Saleh Haggar, ya ce rundunar Operation Haskanite sun fatattaki mayakan.

Gwamnatin Chadi ta ce babu burbudin mayakan Boko Haram da ya rage a cikin kasarta.

Yankin ya ci gaba da zama matattarar masu dauke da makamai, inda ayyukan ‘yan ta’adda da suka mamaye yankin Arewa maso Gabashin Najeriya tun daga shekarar 2009 ya daidata dubban mutane.

Ministan sadarwa na kasar Chadi, Boukar Michel ya ce an bar kasarsa ita kadai take fafatawa a wannan yaki da masu tayar da kayar baya.

"Me yasa aka bar Chadi ita kadai a fagen fama da masu dauke da makamai?" in ji Boukar Michel.

Ya ce me ya sa wadannan 'yan gudun hijirar, wadanda suka rasa matsugunansu, ba su sami wani taimako daga kasashen duniya ba? Me ya sa ba a kula da su ta hanyar jin kai?

Gwamnatin Chadi dai ta yi barazanar ficewa daga rundunar tsaron yankin da ke yaki da ta'addanci.

An kafa rundunar hadin gwiwa ta kasa da kasa MNJTF a shekarar 2015 wadda ta kunshi kasashen Chadi, Najeriya, Nijar, da Kamaru, inda kowannen su ke bayar da gudunmawar sojoji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)