Chadi ta bayarwa Faransa makonni biyu ta gaggauta janye sojojinta cikin ƙasar

Wasu majiyoyi na kusa da gwamnatin Faransa ne suka tabbatar da cewa Paris ta samu wasikar Chadi kan batun janye ɗaukacin sojojin ƙasar kafin cikar wa’adin na ƙarshen watan Janairu, sai dai Faransa ta ce tana tattauna don ganin ta tsawaita wa’adin.

Bayanai na cewa, wasu manyan jami’an sojojin Faransa, kwashe sama da dakaru dubu guda da kayan aiki masu tarin yawa daga ƙasar ta tsakiyar Afirka cikin makonni biyu kachal na da matukar wuya.

Ana kallon matakin gwamnatin Chadi na yanke alakar tsaro da Faransa, a matsayin wata hanyar gayyatar Rasha, to sai dai  Shugaban ƙasar Mahamat Deby ya bayyana cewa ƙasar ba ta da niyyar karkata ƙawancenta na tsaro ga wata ƙasa bayan matakinta na katse alaƙar hadin gwiwar soji da Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)