Wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen kasar Chadi ta fitar ta ce kasar da ke zama babbar abokiyar kawancen kasashen Yamma a yakin da ake yi da mayakan ta’addanci a yankin, tana son tabbatar da cikakken ikonta bayan sama da shekaru sittin da samun 'yancin kai.
Sanarwar ta ci gaba da cewa an yanke shawarar kawo karshen yarjejeniyar hadin gwiwar tsaro da aka sabunta a shekarar 2019.
A baya dai kasar Chadi ta yi ayyukan hadin gwiwa da sojojin kasashen yammacin duniya, amma a baya-bayan nan ta matsa kaimi wajen kara kusantar kasar Rasha.
Tuni dai hukumomin sojan kasar suka soma hulda a bangarori da dama da kasar Rasha, wacce ta girke sojojin haya a sassan yankin Sahel.
Kawo yanzu dai babu wata alama da ke nuna cewa an baiwa gwamnatin Faransa sanarwar matakin, ko da yake a wannan mako jakadan kasar ya gabatar da wani rahoto mai dauke da shawarwari kan yadda Faransa za ta rage yawan sojojinta a kasashen Chadi, Gabon da kuma Ivory Coast, inda ta tura dubban sojoji.
A halin yanzu, sojojin Faransa kusan dubu guda ne hadi da jiragen yaki, aka girke a kasar Chadi da ke yankin Tsakiyar Afirka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI