Chadi ba ta da shirin ƙulla ƙawancen tsaro da kowacce ƙasa- Deby

Chadi ba ta da shirin ƙulla ƙawancen tsaro da kowacce ƙasa- Deby

Wata sanarwa da gwamnati Chadi ta fitar ta ruwaito shugaban ƙasar Janar Mahamat Idriss Deby na bayyana katse ƙawancen tsaron da Faransa a Alhamis ɗin da ta gabata, sai dai ya kawar da duk wani shirin maye gurbin uwar goyon ta Chadi da wata ƙasa ta daban.

Deby ya ce matakin na da nufin sake mayar da hankali kan dangantakar Chadi da Faransa kan wasu fannonin daban saɓanin tsaro, da ɓangarorin biyu suka shafe shekaru suna taimakekeniyar juna.

A cewar Deby yarjejeniyar soji tsakanin Chadi da Faransa ba ta da amfani a yanzu kuma ya saɓa da hakikanin siyasa da kuma zamanin da ake.

A baya-bayan nan Deby na nesanta Chadi da Faransa a batutuwa da dama wanda ya sanya fargabar yiwuwar ƙasar ta bi sahun takwarorinta na Sahel wajen barranta da Paris duk da kasancewar ta wadda ta yi musu mulkin mallaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)