Cece-kuce ya ɓarke a Kamaru bayan hukumar zaɓe ta fitar da adadin masu kaɗa kuri’a

Cece-kuce ya ɓarke a Kamaru bayan hukumar zaɓe ta fitar da adadin masu kaɗa kuri’a

Kundin wanda aka sabinta  a ƴan tsakanin nan, ya kunshi ƴan kasar su kusan miliyan 8 da kuma mazauna ketare dubu 26 da 800 da aka yi wa rijista.

ƙwararre kan harakar da ta shafi zabe, Hubert Kamga ya ce hasashen hukumar Elecam ya yi hannun riga da wanda da jami’iuyun siyasar suka fitar, inda suka ce adadin masu kada ƙuri’a zai iya haura miliyan 15.

Yayin da ya rage kusan watanni 7 a yi zaɓe, Hubert ya buƙaci ƴan kasar su ƙara azama domin ganin adadin ya kai mutum miliyan 10 a kundin masu kaɗa kuri’a

Ƙwararren ya ƙara da cewa, ya da ce shugaban kasar Paul Biya ya samar da wani ƙudiri na musamman domin tilastawa kowane ɗan ƙasa fita kaɗa kuri’a.

Tuni dai bangare ƴan adawa ya soki tsarin da bayyana da mai cike da kura-kurai la’akari da yadda bai ɗauki muradun ƴan kasar dake zaune a ketare da muhimmancin gaske ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)