Cavusoglu: Mun kwashe Turkawa daga yankin Tigray zuwa Addis Ababa

Cavusoglu: Mun kwashe Turkawa daga yankin Tigray zuwa Addis Ababa

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu ya bayyana cewar sun kwashe Turkawa da rikicin yankin Tigray na Itopiya ya rutsa da su zuwa Addis Ababa Babban Birnin Kasar.

Cavusoglu ya fitar da sanarwa ta shafinsa na Twitter cewar game da Turkawan da rikicin yankin Tigray ya rıtsa da su, nan da wani dan lokaci za su hadu da iyalansu a Turkiyya.

Cavusoglu ya ce ya tattauna ta wayar tarho da Turkawan da rikicin ya rutsa da su a Tigray, kuma Turkiyya na tare da su a koyaushe.

A ranar 3 ga Nuwamba ne mayakan TPLF da ke shugabantar yankin Tigray suka kai hari kan sojojin Itopiya. Firaministan Itopiya Abiy Ahmed ya sanar da daukar matakin yakar TPLF a ranar 4 ga Nuwamba.

 


News Source:   ()