Cabral Libii zai sake tsayawa takara a zaben shekarar 2025

Cabral Libii zai sake tsayawa takara a zaben shekarar 2025

Dan siyasar kuma mawallafi ya na mai bayyana cewa an kawo karshen matsalar yan kamaru,ya kuma bukaci yan kasar sun bashi goyon bayan da ya dace a wannan shiri nasa na sake neman kujerar shugabancin kasar ta Kamaru.

Gaban duban yan kasar, Cabral Libii  daya bayan daya ya na mai kawo Karin haske ga masu ra’ayin siyasar sa, Cabral Libii  y ana mai cewa yan kasar ta Kamaru sun gaji.

Shugaban Kamaru a wurin zabe Shugaban Kamaru a wurin zabe © AFP

Kamaru na bukatar yan siyasa da suka jajirce da kuma za su iya kawo sauyin da ya dace a fanonin da suka jibanci kiwon lafiya, tarer da gina asibitoci,bangaren ilimi da kuma baiwa matasa damar amfana da sabin hanyoyin sadarwa na zamani wanda zai taikmaka musu nan gaba  da nufin sake dawo da Kamaru sahun kasashe da aka sani a Duniya.

'Yan Kamaru suna sa ran samun gwamnati ko hukuma da za ta kare su da kuma ba su damar bunkasa basirarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)