Burundi ta kori ma'aikatan WHO daga kasar

Burundi ta kori ma'aikatan WHO daga kasar

Gwamnatin Burundi da ke Gabashin Afirka ta kori wasu ma'aikatar Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya (WHO) su 4 daga kasar bayan aiyana su a matsayin mutanen da ba ta bukata a kasarta.

Sanarwar da Ma'aikatar Harkokin Wajen Burundi ta fitar ta ce ai aike da rubutaccen sako ga WHO inda aka bukaci Wakilin Hukumar a kasar Walter Kazandi Mulombo tare da wasu kwararru 3 da suka hada da Daniel Tarzy, Ruhana Mirindi Bisimwa da Jean Pierre Mulunda Nkata da su bar kasar nan da 15 ga Mayu.

Sakon ya bayyana cewar wadannan mutane ne da ba a bukatar su a Brundi.

Ana zargin WHO da tsoma baki tare da rikita al'amura a Burundi da za ta gudanar da zaben Shugaban Kasa, 'yan Majalisar kasa da na jihohi a ranar 20 ga Mayun 2020.

A kafafan sada zumunta na yanar gizo na Burundi an goyi matakin da gwamnatin kasar ta dauka.

A Burundi duk da mutuwar mutum 1, warkewar wasu 7 da kuma cigaba da kula da wasu 7 da Corona ta kama, ana ci gaba da yakin neman zabe a kasar.

 


News Source:   www.trt.net.tr