Wannan mataki na Burundi babban koma baya ne ga dakarun Sojin Congo waɗanda ke ƙoƙarin kange mamayar da mayaƙan na M23 ke ci gaba da yiwa sauran sassan ƙasar.
Sai dai tuni kakakin ma’aikatar tsaron Burundi ya musanta wannan batu a wani saƙo da ya wallafa a shafin ma’aikatar na X inda ya bayyana cewa har yanzu Sojojin ƙasar na cigaba da aiwatar da aikin da ya kai Congo na fatattar mayaƙan M23.
Wani Sojin Burundi ya tabbatar da cewa mota guda ce ta iso kan iyaka maƙare da sojojin ƙasar da suka taso daga kudancin Kivu kuma wani ɓangare ne na dakarun da ke bayar da kariya ga Kavumu.
Tsawon shekaru Sojin Burundi suka shafe suna aikin yaƙi da ƴan tawayen Burundi masu hijira a Congo, gabanin su karkata zuwa taimakawa Sojin ƙasar don fatattakar ƴan tawayen M23.
Wannan bayanai na janyewar dakarun Burundi na zuwa ne a dai dai lokacin da hukumar kare haƙƙin ɗan adam ta Majalisar ɗinkin duniya ke zargin mayaƙan na M23 da kisan tarin ƙananan yara a lokacin da suka ƙwace manyan birane biyu na lardin Kivu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI