Burkina Faso na sahun ƙasashen Mali da Nijar waɗanda suka fice daga ƙungiyar ECOWAS cikin watan Janairun shekarar nan bayan takunkuman da ƙungiyar ta ƙaƙaba musu biyo bayan juyin mulin Soji.
Tsawon lokaci aka ɗauka ana ƙoƙarin dawo da ƙasashen 3 cikin ƙungiyar ko da ya ke sun yi tsayuwar gwamen jaki.
Ministan tsaron Burkina Faso Mamadou Sana lokacin da ya ke gabatar da sabon fasfon ya bayyana cewa tun cikin watan Janairu ba sa tare da ECOWAS kuma fitar da sabon fasfon na nuna cewa kai tsaye basu da shirin komawa cikin ƙungiyar.
ECOWAS ta bayyana matakin ƙasashen 3 a matsayin barazana ga tsaro da ƴancin mutane miliyan 400 da ke rayuwa ƙarƙashin inuwar ƙungiyar wadda aka kafa shekaru 50 da suka gabata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI