Da daman a ganin sabon fasfon na AES zai kasance wani tsanin samar da ci gaba da kuma hadin kai a tsakanin kasashen uku, musamman yadda aka ga ficewarsu daga ECOWAS.
A birnin Ouagadougou, jama’a da dama ne suka bayyana fatan fasfon na AES zai taimaka wajen kawo karshen labaran karyar da ake yadawa kan kasar, inda da dama ke ganin hakan zai taimaka bayyana irin ci gaban da kasar ke da shi a fannoni da dama.
A farkon makon nan ake sa ran za a ci gaba da samar da fasfon ga ‘yan kasar, abin da zai kasance guda daga cikin manufofin kungiyar AES da ta ce za ta aiwatar, domin hadin kan kasashen.
Sai dai akwai wadanda suka diga ayar tambaya kan wannan sabon tsari, yayin da suke ganin ficewar kasar daga ECOWAS zai iya haifar musu da kalubalen shiga kasashe mambobin kungiyar.
Jama’ar wadannan kasashe, musamman Burkina Faso na fatan cewa, samar da wannan tsari zai saukakawa harkokin tafiye-tafiyensu da kuma kasuwanci a tsakanin Mali da kuma Nijar.
ECOWAS dai ta bayyana cewa, kofa a bude take ga wadannan kasashen a duk lokacin da suka sauya shawara, har ma ta bukaci kasashe mambobinta da su ci gaba da kallon mambobin AES din a matsayin yadda suke a baya, kama daga fuskar kasuwanci, shige da fice da kuma hadin kai.
Amma kasashen uku na ganin hanyar da suka dauka, tamkar samar da ‘yancin kai ne, musamman a fannoni da dama.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI