A ranar Litinin ɗin makon jiya 23 ga watan Satumba ne gwamnatin Sojin Burkina Faso ta bayyana cewa ta daƙile wani yunƙuri na kifar da ita daga mulki, batun da wasu ke ganin ta yi amfani da salon ne don karkatar da hankalin jama’a game da hare-haren ta’addancin watan Agusta, sai dai a yammacin Lahadi da ta gabata ta fitar da wasu bayanai ciki har da faifan bidiyo waɗanda ta bayyana a matsayin hujjar yunƙurin kifar da gwamnatin.
Wani faifan bidiyo da gidan talabijin mallakin gwamnatin ƙasar ya haska ya nuna wasu mutane 3 ciki har da wani kwamandan rundunar tsaro ta musamman Ahmed Kinda a matsayin jagora, lokacin da suke tattaunawa game da shirin yiwa gwamnatin maƙarƙashiya tare da haddasa hargitsi a cikin ƙasar mai fama da hare-haren ƴan ta'adda.
Ma’aikatar tsaron Burkina Faso na fitar da wannan bidiyo ne bayan kisan tsohon kwamandan wanda bayanai ke cewa ya rasa ransa a lokacin da ya ke ƙoƙarin gujewa bincike mahukuntan ƙasar, inda a jawabinsa gaban kyamara ya bayyana cewa an kame shi ne a birnin Yamai na Nijar ranar 30 ga watan Agustan 2024 lokacin da ya ke dakon wasu mutum biyu su kawo mishi makamai.
Faifan bidiyon ya ci gaba da nuna Kinda na cewa rashin samun mutanen biyu ya tilasta mishi sanar da tsohon jagoran sojin ƙasar Laftanal Kanal Paul Henri Damiba da yanzu haka ke gudun hijira a Lome.
Bayanai sun ce ɗan jarida Serge Mahurin ne ya samarwa Kinda ɗakin kwana a birnin Yamai, inda Kinda ya ci gaba da bayyana yadda shirin nasu ya ƙunshi mutane 150 da makamai sai na’urorin sadarwa don kifar da gwamnatin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI