Wannan mataki na sake tabbatar da aniyar gwamnatin na raba gari da ƙungiyar ta ECOWAS.
Wasu bayanai sun nuna cewa jamhuriyar Nijar ma na shirin fitar da nata sabon fasfo ɗin wanda shima babu tambarin ƙungiyar ta ECOWAS a jikinsa.
Da yake ƙarin haske ministan harkokin tsaron ƙasar Mahamadou Sana ya ce wannan na cikin shirin ƙasar na raba kanta da duk wani abu da ya shafi ƙungiyar ta ECOWAS.
Wannan mataki na zuwa ne duk da gargadin da ƙungiyar ta yi na cewa matakin ƙasashen Nijar, Mali da kuma Burkina Faso na ficewa daga cikinta zai shafi mutane sama da miliyan 400 da harkokin kasuwanci da tattalin arzikinsu.
Sai dai a cikin jawabin da gwamnatin tayi a hukumance bata fayyace lokacin da za’a fara amfani da fason wajen tafiye-tafiye ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI