
Ministocin harkokin wajen ƙawancen AES ne suka ƙaddamar da tutar a wani taro ƙarƙashin jagorancin firmainistan Mali, Abdoulaye Maiga, bayan da shugabannin ƙasashen uku suka amince da ita, kamar yadda wata sanarwa daga ofishin yaɗa labaran ƙawancen ta bayyana.
Tutar ta AES ɗin kalar kore ce mai ɗauke da tambarin ƙungiyar a tsakiya.
Sanarwar ta ce kalar kore alama ce ta fata na gari, cigaba da kuma sauyi, kamar yadda sanarwar ƙungiyar ta yi bayani, inda ta ƙara da cewa kalar na waƙiltar ɗimbim albarkatun ƙasa da ƙasahsn ke da su.
Ƙasashen uku, waɗanda ke ƙarƙashin mulkin soji, kuma ke fama da matsalar ayyukan ‘yan ta’adda da sauran matsaloli, sun sanar da ficewa daga ƙungiyar ECOWAS a ranar 28 ga watan Janairu shekarar 2024. Kuma a ranar 29 ga watan Janairun wannan shekarar ta 2025 ce aka amince da ficewar tasu a hukumance, bayan sama da shekara guda ana tankiyar diflomasiyya.
Ƙasashen da ke ƙarƙashin gwamnatocin soji, sun zargi ECOWAS da kasancewa karnukan farautar Faransa, tsohuwar uwargiyarsu.
A ƙarshen watan Janairu ne kuma ƙasashen suka samar da fasfo ɗinsu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI