Burkina: Ƴan jarida sun buƙaci bayani kan abokan aikinsu da suka ɓace

Burkina: Ƴan jarida sun buƙaci bayani kan abokan aikinsu da suka ɓace

Ƴan jaridar huɗu na Burkina Faso da suka bace ne a lokuta mabambanta a cikin watan Yuni a  Ouagadougou babban birnin kasar, su ne, Serge Atiana Oulon da Kalifara Séré da Alain Traore da kuma Adama Bayala, kuma ana zargin gwamnatin ƙasar ce ta yi awon gaba da su.

Tun bayan da shugaban rikon kwarya, Ibrahim Traoré, ya ya yi juyin mulki a shekarar 2022, kungiyar CPJ ta tattara wasu bayanai wadda a ciki ta gano tabarbarewar harkokin 'yancin 'yan jarida a ƙasar, da suka hada da rufe kafafen yada labarai, korar wakilai da ke aikewa da rahotanni daga kasashen ketare, da kuma kokarin kawar da 'yan jarida masu tsatsauran ra’ayi.

Sai dai ƙungiyar kwararrun ƴan jarida ta ƙasa-da-ƙasa, RSF ta bayyana cewa Dole ne mahukuntan Burkina Faso su yi duk mai yiwuwa wajen fitowa, tare da tabbatar da tsaron 'yan jaridar.

Wanna na zuwa ne daidai lokacin da hukumar kula da kafafen yaɗa labarai ta ƙasar ta  ba da tabbacin cewa kwararrun kafafen yada labarai a Burkina Faso ne kaɗai za su iya ci gaba da aiki ba tare da wata tantancewa ba, saboda muhimmancin labaran da suke yadawa, a cewar Angela Quintal shugabar hulumar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)