Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kira ga shugabannin kasashen Yammacin Afirka da su hada kai waje guda don yaki da ta'addanci.
Kakakin Shugaba Buhari Malam Garba Shehu ya fitar da sanarwa bayan harin da aka kaiwa wasu kauyukan Nijar da ke iyaka da Mali tare da kashe mutane kusan 100.
Shehu ya soki harin inda ya ce "Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kira ga shugabannin kasashen Afirka da su hada kai wajen yaki da ta'addanci."
Shehu ya yi nuni da cewar, sun dimautu da yadda aka kashe fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba, kuma yankin Sahel na fama da aiyukan ta'addanci wanda idan ba a dauki matakan da suka kamata ba, to zai game ko'ina.
Kakakin ya ci gaba da cewa, bayan kashe Shugaban Libiya Muhammad Gaddafi, kasashen yankin da suka hada da Najeriya, Nijar, Mali da Chadi sun fada mummunan yanayin tsaro, kuma bayan haka makaman kasar sun fada hannun 'yan ta'adda.