Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya tattauna da ministan harkokin wajen Amurka Antony Blinken ta yanar gizo.
A tattaunawar Buhari ya yi kira ga Amurka da ta maido da Cibiyar Dakarun Afrika ta Amurka (AFRICOM) daga garin Stuttgart dake Jamus zuwa Afirka.
Haka kuma Buhari ya yi kira ga hukumomin kasa da kasa da taimakawa yammacin Afrika wajen samar da tsaro.
Ya kara da cewa matsalar tsaro a Najeriya na cigaba da damuwarmu. Haka kuma wannan matsalar na kara gurbata sabili da rashin tsaron da yankunan Sahel, tsakiya da yammacin Afrika da ma yankin tafkin Chadi ke ci gaba da fama dashi.
aa/tuğba