Bozize ya zama shugaban 'yan tawayen CPC

Bozize ya zama shugaban 'yan tawayen CPC

A Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya an sanar da cewa, hambararren Shugaban Kasar Francois Bozize ya zama shugaban 'yan tawaye da suka baiwa kansu sunan Kawancen Masoya Kasa da Kawo Chanji (CPC).

Bayanan da kafafan yada labarai na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya suka fitar sun rawaito kakakin CPC Serge Bozanga na fadin cewar, Bozize ya amince da bukatar kawancen kungiyoyin 'yan tawaye 6 na ya zama shugabansu karkashin inuwar CPC.

Kungiyoyin 'yan tawayen da suka hada kai suka kafa CPC sun hada da: 3R, UPC, MPC, FPRC da kuma kungiyar Kiristoci ta Anti-Balaka.

A ranar 27 ga Disamban 2020 ne kotun kolin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta ki amincewa da tsayawa takarar Shugaban Kasa na Francois Bozize sakamakon zargin aikata laifukan yaki da Majalisar Dinkin Duniya ta ke yi masa, hakan ya janyo fara rikici tsakanin sojojin gwamnati da 'yan tawaye masu dauke da makamai a ranar 18 ga Disamba.

Kawancen CPC sun fara kai hare-hare don kwace iko da Bangui Babban Birnin Kasar, wadda kusan kaso 80 dinta ke karkashin ikon 'yan tawayen.

Gwamnati da Majalisar Dinkin Duniya sun dorawa Bozize alhakin rikicin da ake fuskanta, suna kuma zargin sa da yunkurin yin juyin mulki.


News Source:   ()