Boko haram ta sake hallaka sojojin Chadi da dama da suka hada da manyan hafsoshi

Boko haram ta sake hallaka sojojin Chadi da dama da suka hada da manyan hafsoshi

Shugaban kasa Mahamat Idris Deby ne ya bayyana kashe sojojin a sakon da ya wallafa a shafinsa na facebook ba tare da karin bayani a kan lamarin ba.

Deby ya bayyana ta'aziyarsa ga 'yan uwa da iyalan sojojin da ya ce sun kwanta dama wajen kare kasarsu a fafatawar da suka yi, tare da fatar samun sauki ga wadanda suka samu raunuka lokacin arangamar.

Wannan fafatawa itace ta baya bayan nan, baya ga wadda akayi a karshen watan Oktobar da ta gabata, wanda ya yi sanadiyar hallaka sojojin kasar 40, wanda shi da kan shi shugaban ya jagoranci kai farmakin daukar fansa tare da barazanar janye sojojin kasar daga rundunar hadin kai ta MNJTF.

Shugaban rundunar sojin Chadi ya sanar da arangamar da sojojin kasar suka yi da mayakan boko haram a ranar asabar da ta gabata, tare da alkawarin karin haske akan irin ta'addin da suka yi.

Rahotanni sun ce an yi fafatwar ce a tsibirin Karia dake arewa maso yammacin tafkin Chadi.

Wani babban jami'in sojin kasar ya shaidawa kamfanin dillancin labaran AFP cewa manyan jami'ansu da dama sun kwanta dama a fafatawar.

Rikicin boko haram da ya barke a Najeriya a shekarar 2009 ya yi sanadiyar hallaka mutane sama da 40,000, yayin da sama da miliyan 2 suka tsere daga muhallinsu

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)