Boko Haram ta kaiwa rundunar sojoji hari a Najeriya

Boko Haram ta kaiwa rundunar sojoji hari a Najeriya

A harin da 'yan ta'addan Boko Haram suka kaiwa tawagar motocin sojoji a arewa maso gabashin kasar Najeriya mutum 19 sun rasa rayukansu.

Kamar yadda kafafen yada labaran cikin gidan kasar Najeriya suka rawaito, kungiyar Boko Haram ta kaiwa tawagar sojoji hari a Gudumbali dake yankin tafkin Chadi.

A harin sojoji 15 da 'yan sa kai 4 sun rasa rayukansu.

Mai magana da yawun rundunar sojan Najeriya Muhammed Yerima da yake tabbatar da kai harin ya bayyana cewa sojoji da dama sun raunana.

Boko Haram da ta bulla a Najeriya a 2000 ta kuma rikide ta fara kai miyagun hare-hare a 2009 ta yi sanadiyar rasa rayukan fiye da mutum dubu 20.

Lamarin kuma ya yi sanadiyar rasa matsugunan dubun dubatan mutane.


News Source:   ()