Kungiyar ta'addar Boko Haram ta sake kai wani harin bindiga a arewa maso gabashin Najeriya tare da kashe mutum 30.
Danagane ga bayanan da suka fito daga kafafen yada labaran cikin gidan kasar wani jami'in tsaro da ya nemi a boye sunansa ya tabbatar da cewa kungiyar Boko Haram ta kai hari a kauyen Gubio dake jihar Borno.
Jami'in ya bayyana cewa a harin ta kashe mutum 30 tare da raunana wasu da dama.