Kungiyar ta'addar Boko Haram ta kai hari arewa masu gabashin Najeriya inda ta hallaka mutane 69.
Dangane ga labaran da suke fitowa daga kafafaen yada labaran kasar mambobin Boko Haram sun bayyyana a kauyen Foduma Kolomaiya dake jihar Borno inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi.
A harin sun kashe mutum 69 da kuma raunana wasu da dama, sun kuma kone gidaje da dama da kuma hallaka shanu fiye da 300.
Mai magana da yawun rundunar sojan Najeriya Musa Sagir kawo yanzu bai cewa manema labarai uffan ba game da harin.
Shugaban hafsan sojojin Najeriya Janar Tukur Yusuf Buratai a ranar Litini ya bayyana cewa a cikin wata daya da ta gabata an kashe mamabobin Boko Haram 429a hare hare da dama.
Daga shekarar 2000 kawo yanzu a Najeriya da Boko Haram ta bayyana ta hallaka fiye da mutum dubu 20 daga shekarar 2019 da ta fara kai munanan hare-hare.