Boko Duma zai ƙara albashin ma'aikatan Botswana tare da inshorar lafiya ga kowa

Boko Duma zai ƙara albashin ma'aikatan Botswana tare da inshorar lafiya ga kowa

A jawabinsa na karɓar aiki Duma Boko mai shekaru 54 ya sake nanata ƙudirin na ruɓanya mafi ƙarancin albashin ma’aikata da kuma gbatar da sabon tsarin inshorar lafiya da kowanne ɗan ƙasar zai amfana.

Ƙarƙashin sabon tsarin na shugaba Boko kowanne ma’aikaci zai riƙa karɓar kuɗin ƙasar pula dubu 4 dai dai da dalar Amurka 300, wanda na daga cikin alwashin da shugaban ke ci gaba da nanatawa.

A cewar Duma Boko gwamnatinsa na da ƙwarin gwiwar shigowar masu zuba jari baya ga ƙulla alaƙa da kamfanonin haƙar ma’adinai da nufin baza komar tattalin arziƙin ƙasar saɓanin dogaro da iyakar lu’u lu’u.

Zaɓen na Botswana dai ya bayar da mamaki matuƙa musamman ganin yadda aka fitar da jam’iyyar shugaba Mokgweetsi Masisi ta BDP daga office duk da kasancewarta wadda ke mulkin ƙasar tun daga 1966 wato tun bayan samun ‘yancin kan ƙasar daga Birtaniya.

Tuni dai Masisi ya taya murna ga ɓangaren adawar, inda yayin wani taron manema labarai jim kaɗan bayan rashin nasararsa ya bayyana cewa shi da jam'iyyarsa sun ginu ne a tsantsar demokradiyya wanda ya sanya dole su girmama ra'ayin mutane kamar yadda sakamakon ya nuna.

An ga dai yadda magoya bayan Duma galibi matasa ke ci gaba da shagulgulan murna a titunan ƙasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)