Bincikenmu ya gano cewa an aikata laifukan yaki a Libya - ICC

Bincikenmu ya gano cewa an aikata laifukan yaki a Libya - ICC

Kharim Khan ya shaidawa Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya cewa, a shirye yake yayi aiki da gwamnatin Libya da al’ummar ƙasar, da sauran ƙasashe mambobin kotun ta ICC dama waɗanda ba mambobi wajen kamo waɗanda ake zargi.

Tun na watan Oktoban daya gabata ne dai kotun ta bada umarnin kamo Abdelrahim al-Kani da Makhlouf Douma da Nasser al-Lahsa da Mohammed Salheen da Abdelbari al-Shaqaqi da kuma Fathi al-Zinkal.

Khan ya ce uku daga cikin waɗanda ake zargin ƴaƴan ƙungiyar Al Kaniyat ne, yayinda ragowar ukun jami’an tsaron Libya ne.

Ita dai kotun ta ICC bata da jami’an ƴan sanda nata, sai dai ta dogara ne wajen amfani da ƙasashe mambobinta 124, wajen kamo waɗanda take nema ruwa a jallo.

Babban mai shigar da ƙarar ya ce ya gana da waɗanda aka ci zarafinsu da suka fito daga yankin Tarhuna, kuma sun shaida masa irin yadda aka azabtar da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)