Shugaban ma’aikata na fadar gwamnatin Kamaru Samuel Mvondo Ayolo ne ya wakilci shugaban ƙasarsa Paul Biya a birnin Paris na kasar Faransa domin mika rahoton ga shugaba Emmanuel Macron ranar Talata.
Tun a watan Fabrairun shekarar 2023 ne aka kafa kwamitin kwararru daga kasashen biyu, ƙarkashin jagorancin masanin tarihin Faransa Karine Ramondy da mawaƙin Kamaru Blick Bassy, domin fayyace rawar da Faransa ta taka a Kamaru daga shekarar 1945 zuwa 1971.
Anata bangaren, Faransa za ta gabatar da nata rahoton ga bangaren Kamaru a ranar 28 ga watan Janairu, a Yaoundé.
Shugaban na Faransa Emmanuel Macron ne dai ya bukaci bincikar lamarin, a wani bangare ne neman sabuwar dangantaka da Afirka.
Wannan ya biyo binciken da ya bukaci a gudanar kan rawar da Faransa ta taka a kisan kiyashin Tutsi a Rwanda, da kuma lokacin mulkin mallaka da kuma yakin adawa da ƴan kan ƙasar Aljeriya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI