Biden ya jaddada aniyarsa ta kulla alaka mai ɗorewa da ƙasashen Afirka

Biden ya jaddada aniyarsa ta kulla alaka mai ɗorewa da ƙasashen Afirka

Biden dai ya kasance shugaban Amurka na farko da ya taɓa kai ziyara ƙasar ta Angola, inda ya nuna farin cikinsa da hakan.

Ina matukar alfahari da kasance wa shugaban Amurka na farko da ya ziyarci Angola kuma ina matukar alfahari da duk wani abu da muka yi tare don kawo sauyi a dangantakarmu.

Sai dai ana ganin Biden ya kai ziyarar ce don rage ƙarfin faɗa aji da abokiyar hamayyarta ta fuskan kasuwanci China ke samu a nahiyar, musamman yadda Amurka ta maida hankali wajen sabunta layin dogon da ya haɗa ƙasashen Zambia da Congo da kuma Angola, wanda zai lakume dala biliyan 3.

A gobe Laraba ne dai shugaba Biden zai kai ziyara yankin Lobito, wajen da ake aikin sabunta layin dogon da zai wuce har zuwa gaɓar tekun Atilantika.

Haka nan zai ziyarci babban gidan adana kayan tarihin Angola da aka yi cinikin bayi, kuma ake saran ya gabatar da jawabi game da tarihi kan hakan da kuma alfanun da ƙasashen biyu za su samu game da ziyarar.

Shekaru da dama da suka gaba, Amurka ta ƙulla alaka da ƙasashen Afrika a ɓangarorin kasuwanci da tsaro da kuma bada agaji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)