Biden ya bai wa Afrika gudunmuwar rigakafin cutar ƙyandar biri miliyan daya

Biden ya bai wa Afrika gudunmuwar rigakafin cutar ƙyandar biri miliyan daya

Shugaba Biden ya bayyana hakan ne a lokacin babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya da ke gudana a birnin New York, inda ya buƙaci sauran ƙasashe su yi koyi da su.

A cikin watan Agustan da ya gabata ne dai Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta sanya dokar tabaci akan cutar ta ƙyandar biri, wanda shi ne karo na biyu a cikin shekaru biyu, sakamakon bullar wani sabon samfarin cutar da aka samu a Jamhuriyar Dimukaradiyar Congo, wacce ta bazu zuwa wasu ƙasashe da ke makwabtaka da ita, da ma wasu da ke wajen nahiyar, ciki har da India.

A cewar wani bincike da Kamfanin Dillancin Labaran Reuters ya gudanar, ƙasashe masu karfi sun mallaki miliyoyin allurar rigakafin cutar, sai dai gudunmuwar da suke bayar wa ta gaza abinda ake buƙata wajen yaki da cutar.

Ko a makon da ya gabata, sai da haɗakar Gavi da ke samar da rigakafin cututtuka, ta sanar da bada gudunmuwar rigakafin cutar dubu dari biyar, don dakile ta baki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)