Shugaban Kasar Amurka Joe Biden ya tattauna ta wayar tarho da Shugaban Kasar Kenya Uhuru Kenyatta.
A tattaunawar, Biden ya shaida cewa, suna son hada kai tare da aiki da Kenya a yankunansu.
Fadar White House ta sanar da cewa, tattaunawar ta Biden da Kenyatta ta jaddada muhimmancin alakar Amurka da Kenya.
An bayyana cewa, domin tabbatar da tsaro a yankunansu, Amurka ta yanke hukuncin yin aiki tare da Kenya.
Biden ya yaba irin jagirancin da Kenya ke yi a Gabashin Afirka, cigaban tattalin arziki, yaki da ta'addanci da sauyin yanayi da ta ke yi.
Shugabannin sun kuma tabo batun rikicin yankin Tigray na Itopiya.