Benin ta yi watsi da zargin da Nijar ta yi mata na taimakawa ƴan ta'adda

Benin ta yi watsi da zargin da Nijar ta yi mata na taimakawa ƴan ta'adda

Da yake martani kan zargin ranar Litinin Ministan harkokin wajen Benin, Shegun Bakari, ya gayyaci babban jami’i a ofishin jakadancin Nijar a Benin domin yi musu bayani kan wadandan zarge -zarge da ya kira maras tushe balle makama.

A ranar kirsimeti wato 25 ga watan Disamba ce Shugaban mulkin sojan Nijar ya zargi Benin da hannu a ayyukan dagula al'amuran kasarsa, yana mai cewa ƙasar sayan kayayyakin tare da rabawa ƴan ta'adda.

Cote d'Ivoire

Rundunar Sojin Cote d'Ivoire ma ta fitar da makamaicin wannan sanarwa ta watsi da zargin da mahukuntan sojin Nijar ta yi masu na kafa sansanin horas da ƴan ta'adda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)