Benin ta kama wasu da ake zargi da shirya juyin mulki a kasar

Benin ta kama wasu da ake zargi da shirya juyin mulki a kasar

Bayanai daga Elonm Mario Metonou mai shigar da kara na kotun hukunta laifukan tattalin arziki da ta'addanci a Benin (CRIET) wata kotu da shugaban kasar Patrice Talon ya samar yan lokuta da hawansa karagar mulki, mai shigar da kara yayin  taron manema labarai a jiya ya na mai bayyani fila fila cewa,ta hannun tsohon Ministan wasannin kasar  Oswald Homeky aka bude wani asusun ajiya da sunan kwamandan rundunar tsaro a Abidjan ,inda aka zuba wasu makudden kudade,daga bisali aka shirya wasu jakunan kudi na kusan bilyan daya da rabi na cfa  da aka saka cikin wata mota ta ministan wanda jami’an tsaro suka cafke  cikin daren talata.

An kama Oswald Homéky, tsohon ministan wasanni ne a daren ranar Litinin zuwa Talata da misalin karfe 1 na safe yayin da ya ke kokarin baiwa Djimon Dieudonné Tévoédjrè, kwamandan tsaron kasar jakunkuna shida.

An kuma Olivier Boko, wanda tsohon abokin shugaban kasar Patrice Talon ne a daren ranar Litinin zuwa Talata a Kwatanu.

Wani dan kasar ta Benin dake bibiyar abinda ke faruwa yanzu ya na mai cewa.

A shekarar 2026 ne shugaban kasar Patrice Talon zai kawo Karshen wa’adin shugabancin sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)