Benin ta amince da sabon jakadan da Jamhuriyar Nijar ta tura ƙasarta

Benin ta amince da sabon jakadan da Jamhuriyar Nijar ta tura ƙasarta

A ranar Larabar da ta gabata ne dai Jamhuriyar Benin ta amince da sabon jakadan da gwamnatin sojin Nijar ta tura ƙasar, yayin da tuni Nijar ɗin ta sake karɓar Jakadan makwafciyar tata a farkon watan Satumba.

A farkon watan Yuli ne dai sojojin da ke mulkin Jamhuriyar Nijar su ka amince su tattauna da gwamnatin Benin, ƙarƙashin jagoraancin tsaffin shugabannin ƙasar biyu, don taimakawa wajen maido da dangantaka biyo bayan juyin mulkin shekarar da ta  gabata, wanda ya kai gab rufe kan iyaka, lamarin da ya sa Benin ɗin ta dakatar ɗaukar ɗanyen man Nijar daga gaɓar tekunta.

Bayuan tattaunawa da shugaban gwamnatin sojin Nijar Janar Abdourahamane Tiani da saffin sshugabannin Benin,  Thomas Boni Yayi da Nicephore Soglo a ranar 24 ga watan Yuni, gwamnatin Nijar ta fitar da wata sanarwar da ke bayyana cewa ta amince da batu maido da dangaantaka tsakaninta da Benin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)