A cikin wata sanarwa da ma’aikatar tsaron ƙasar ta fitar a yau Asabar, ta ce babu wata yarjejeniyar da ta ke da ita da ƙungiyoyin ƴan ta’addan.
Sanarwar ta ƙara da cewa, jami’an tsaron ƙasar na aiki tukuru wajen yaki da ta’addanci, musamman a yankin iyakarta ta Arewaci.
Ma'aikatar tsaron Ghana ta yi watsi da ƙaƙƙausar murya kan yadda ake nuna cewa Ghana ce cibiyar hada-hadar ƴan ta’adda. Ghana na ƙoƙarin yaki da ta'addanci yadda ya kamata tare da abokan huldarta, a yakin da ake yi da ta'addanci a yankin da ma duniya baki daya.
Dama a tsakiyar wannan makon ne Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya yi wani rahoto da ya ce wasu majiyoji 7 ciki har da na jami’an tsaro da kuma difulomasiyar Ghana, na zargin ƙasar da kauda ido kan yadda masu iƙirarin jihadi daga makwabciyarta Burkina Faso, na amfani da iyakarta a matsayin wurin kula da lafiyar mayakansu da kuma samun kayan abinci da man fetue da kayayyakin fashe-fashe.
Ghana na da iyaka mai nisan kilomita dari 6 da Burkina Faso, wacce ke fama da matsalolin ƴan ta’adda da suka kashe dubban mutane tare da raba miliyoyi da muhallansu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI