Mutum daya ya rasa ransa, wasu mutanen 3 kuma sun samu raunuka sakamakon fashewar wani bam da aka binne a gefen hanya a Mogadishu Babban Birnin Somaliya.
Bam din ya fashe a gefen hanya alokacin da motar ma'aikatan lafiya da ke bin diddigin masu dake da Corona ta ke wucewa ta gundumar Karan da safiyar Larabar nan.
Mutum 1 ya rasa ransa, wasu 3 kuma sun jikkata sakamakon fashewar bam din.
An aike da jami'an tsaro zuwa yankin bayan fashewar bam din, babu wanda kuma ya dauki alhakin binne bam din.