Wasu 'yan gudun hijira su 95 da suka tashi daga Afirka zuwa Turai sun yi jiran awanni 30 a kan tekun bayan mika bukatar a zo a kubutar da su.
Shafin Twitter mai suna "Alarm Phone" da ke bibiyar kai-komo da motsin 'yan gudun hijira a tekun Bahar Rum ya sanar da cewar tsawon awanni 30 'yan gudun hijira su 95 suka kira wayar tarho tare da neman a je a kubutar da su a tekun.
Shafin ya bayyana cewar "Wani jirgin ruwan dakon kaya ya tsaya yana kallon su ba tare da bayar da wani taimako ba. Har zuwa yaushe jama'a za su fada hatsarin dilmiyewa a ruwa? Har zuwa yaushe za su rayu?."
Kakakin Ofishin Hukumar Yaki da Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (IOM) na Italiya Flavio Di Giacomo ya yada bayanan na "Alarm Phone" inda ya kuma ce "'yan gudun hijira na jira a kubutar da su a tekun Bahar Rum. Dole a je kubutar da su nan da nan."
A 'yan shekarun da suka gabata ana yawan samun kwararar masu gudun hijira daga Afirka zuwa Turai inda suke bi ta yankunan Libiya, Malta da Italiya.