
Sanarwar da ma’aikatar cikin gida ta kasar ta fitar ta ce, an samu ci gaba a yakin da Maroccon ta ke yi wajen yaki da matsalar kwararar bakin hauren da ke amfani da ita wajen shiga Turai.
A cewar sanarwar kaso 58 na bakin hauren sun fito ne daga Yammacin Afirka, sai kaso 12 daga Arewaci, wato yankin da kasar ta fito kenan inda kaso tara kuma suka fito daga Gabashi da kuma tsakiyar yankin.
Shekarun da aka dauka ana rikice-rikice a ƙasashen yankin Sahel, da rashin ayyukan yi, da kuma matsalar sauyin yanayi musamman a wuraren da ake noma, ya haifar da kwararar bakin haure zuwa Turai, domin neman rayuwa mai inganci.
Marocco da maƙwabciyarta Spain da ta kasance mamba a Ƙungiyar Tarayyar Turai, na fuskantar matsalar kwararar baƙin haure.
Kasar da ke arewacin Afirka, ta jima da kasancewa wata cibiyar yada zango ga bakin haure.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI