Kakakin gwamnatin Chadi Abderaman Koulamallah ya ce maharan 24 ne suka kai harin amma dakarun Sojin ƙasar sun hallaka 18 daga cikinsu.
Koulamallah ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da ya kira jiya alhamis.
Idan ba don hasarar rayukan da aka samu ba, dariya abin zai baka, don gungun zauna gari banza ne kawai dauke da wukake da sauran nau’ikan makamai da ba na yaki ba.
Waɗannan matasa sun fito ne daga wata gunduma dake karkashin garin N’djemena, wannan lamari bashi da wata alaka da boko haram, salon ba na boko haram bane.
Da sannu binciken da aka dorawa mai gabatar da kara alhakin gudanarwa zai tantance ko su wane ne wadannan.
A nawa ra’ayi, wannan ba ta’addanci ba ne, yunkurin ne kawai na wasu mutane matasa da wasu miyagun mutane ke amfani dasu.
Babu wani abu da zai yi barazana ga tsaron kasarmu, hukumomin kasar, ballantana fadar Shugaban kasa. Kawai jama’a su cigaba da harkokinsu kamar yadda suka saba.
A cewar Koulamallah
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI