Babu dan takarar da ya yi nasarar samun kaso 50 cikin 100 na kuri'un da aka jefa a zaben Shugaban Kasar Nijar da aka gudanar a ranar 27 ga Dİsamba wanda hakan ya sanya za a gudanar da zagaye na 2.
Sanarwar da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta fitar ta ce, a zagayen farko tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida Mohamed Bazoum ya samu kaso 39,33 sai mai biye masa baya Mahamane Ousmane da ya samu kaso 17 cikin dari na kuri'un da aka jefa.
Akwai masu jefa kuri'a kusan miliyan 7,4 a Nijar wanda a ranar 27 ga Disamba suka fita rumfunan zabe don zaben Shugaban Kasa da 'yan Majalisar dokoki 171.
A ranar 28 ga Fabrairu Bazoum da Ousmane za su fafata a zagaye na 2.
Baya ga Bazoum da Ousman akwai 'yan takara 28 da suka shiga zaben Shugaban Kasar.
A karon farko a Jamhuriyar Nijar da ta sha fama da juyin mulkin soji, zababbiyar gwamnatin farar hula za ta mikawa wata farar hula mulki.
Shugaba Mai Ci Muhammad Issoufou ya kammala wa'adinsa 2 a saboda haka bai iya sake tsayawa takara ba.
A kananan zabuka da aka gudanar a ranar 13 ga Disamba, Jam'İyyar PNDS Tarayya mai mulki ce ta yi nasara a fadin kasar.