Kusan mako daya da yan adawa suka sanar da wadan bukatu ne sai ajiya juma’a Shugaban kasar Mahamat Idriss Deby ya kira shugabannin jam'iyyun siyasa a domin bayyana cewa za a gudanar da zaben 'yan majalisar dokoki da na kananan hukumomi a ranar 29 ga watan Disamba. Shugaban ya karasa da cewa kasar ta fuskanci ambaliya kuma wannan iftila’I ba zai kawo cikas ga batun zaben kasar na Chadi ba.
Shugaban kasar Chadi Mahamat Idriss Deby Itno AP - Wang ZhaoShugaban Chadi da ke Magana gaban yan siyasa ya na mai fatan ganin kowane daga cikin su ya taka rawar da ta dace don samun nasarar wannan aiki na ceto kasar ta Chadi.
Yan siyasa a gaban Shugaban kasar sun sake nanata fatan ganin an dage zabukan kasar na Chadi ,zabukan da suka hada da na‘yan majalisu da na kananan hukumomi sakamakon ambaliyar ruwa da tuni ta yi sanadin mutuwar kusan mutane 600, kusan mutane miliyan biyu suka rasa matsuguni da kuma gurgunta wani yanki na kasar Chadi,banda hakan daya daga cikin manyan jam’iyyun adawa ta Les Transforamateurs da ta sanar da kauracewa zaben na iya kawo cikas ga baki daya a wannan zabe.
Jagoran yan adawa na kasar Chadi Succès Masra © Carol Valade/RFIHaka zalika wasu daga cikin jam’iyyun siyasa kusan goma sha biyar suka nuna cewa za su kaurace wa zaben, matakin da yanzu kam ya janyo cece-kuce a cikin kawancen jam’iyyu ,masu dafawa Shugaban kasar.
Hakan bai hana daya daga cikin shugabanin jam’iyyun bayyana cewa “Ba mu shirya kwata-kwata ba, na zuwa zaben kasar ta Chadi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI